An bude 2013 da kada gangar siyasa a Najeriya

Goodluck Jonathan
Image caption Wannan lamari ya fara janyo cece-kuce a fagen siyasar kasar

Mazauna birnin Abuja a Najeriya sun shiga sabuwar shekara ta 2013 da wasu hutunan shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan na neman tsayawa takara a shekara ta 2015.

Wakilin BBC a Abuja Ibrahim Isa ya ce an lillika hotunan ne a wasu wurare da za a iya bayyana su da cewar idon jama'a ne kasancewarsu cike da ribibin jama'a a kodayaushe.

Ya kara da cewa wasu an lika su a jikin gine-gine da turakun wutar lantarki da ke tsakiyar tituna, wasu kuma jikin itatuwa aka manna su, kuma da ganin hutunan ka san suna da inganci da nagarta, don haka an kashe nairori wajen yin su.

Tuni dai wasu 'yan jam'iyyun adawa suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan wannan lamari, wadanda ke cewa ba sa tsoron karawa da shugaban kasar a zabe na gaba.

"Ba ma tsoronsa"

Kakakin fadar shugaban kasar Reuben Abati ya shaidawa BBC cewa, shugaba Jonathan ba shi da hannu a lika fastocin, kana kuma bai umarci wasu su fara masa yakin neman zabe ba.

Mista Abati ya jaddada cewa shugaban ya ce a yanzu gwamnatin na maida hankali ne bisa ayyukan raya kasa.

Sannan da sauke nauyin da 'yan kasar suka dora masa, a matsayinsa na shugaban kasa.

"Bara ma ya yi mana bazata da kara kudin man fetur, yanzu kuma sun fito da wannan," a cewar Hon Faruk Adamu Aliyu jigo a jam'iyyar adawa ta CPC.

Wannan ya nuna cewa shi shugaba ne na wani bangare daya, "muna fata, muna roko don Allah Goodluck ya zo ya tsaya.

Kwata-kwata ba ma tsoronsa, abubuwan da suka faru a cikin shekarar da ta gabata, sun isa su nuna wa 'yan Najeriya cewa wannan ba jagora ba ne da ya kamata a bishi," a cewar Faruk Adamu Aliyu.

Yayin da 'yan adawa ke cewa PDP ta gaza, gwamnati karkashin jagorancin shugaba Jonathan na bugun kirji da cewar ta samu nasarori wajen yin shimfidar da za ta hanzarta samar da abubuwan more rayuwa a kasar nan kurkusa

Da wadannan hotuna dai za a iya cewa an fara bude shekara ta 2013 a Najeriya da kada gangar siyasa.

Kuma wannan ya tabbatar da hasashen da wasu masana harkokin siyasa suka yi cewa watakila hankalin shugabanni da 'yan siyasa zai fara rajja'a ga yakin neman zaben shekara ta 2015 tun a farkon 2013.

Kuma masu lura da al'amura na ganin idan haka ta kasance, to da wuya su samu natsuwar aiwatar da ayyukan raya kasa.

Karin bayani