Amurka: Hannayen jari a duniya sun farfado

stock
Image caption Kasa cimma matsaya a Amurka zai shafi kasuwannin jari

Kasuwannin hannayen jari a ko'ina cikin Asiya da Turai sun tashi matuka bayan cimma yarjejeniyar tsakar dare a Amurka wadda ta soke wani jerin babban karin haraji da zaftare kudaden da gwamnati ke kashewa da da zai fara aiki nan take da shigowar sabuwar shekara.

Shugaba Obama na Amurka ya ce ana bukatar karin tashi tsaye don karfafa tattalin arzikin Amurka, bayan yarjejeniyar tsakiyar dare da aka cimma a Washington, wanda ya yi maganin aukawar kasar cikin matsalar kasafin kudi.

Da yake jawabi kafin tashi zuwa Hawaii don ci gaba da hutunsa, shugaban ya ce a shirye yake ya yi sassauci a tattaunawar da ke gaba.

Gabanin sannan dai, majalisar wakilan kasar ta amince da yarjejeniyar da gwamnatinsa da kuma majalisar dattijai suamince ne a kai.

In ba don yarjejeniyar ba, da tilas gwamnati ta yi mummunan tsuke bakin aljihunta, tare kuma da kara haraji a kan duk wani mai biyan harajin.

Hakan kuwa zai iyi sake jefa Amurkar cikin matsalar tattalin arziki.

Karin bayani