Ganawa tsakanin 'yan tawayen Congo da gwamnati

'Yan tawayen M23 na Congo
Image caption Za a gana tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Congo

A yau ne Gwamnatin Jamhuriyar dimokradiyyar Congo da kuma kungiyar 'yan tawaye za su koma don tattaunawa a Uganda.

Sai dai kuma kungiyar 'yan tawayen ta M23 ta ce ba za'a fara duk wata tattaunawa ba har sai an bayyana wani shiri na tsagaita wuta.

Daya daga cikin shugabannin 'yan tawayen Bishop Marie Runiga ya ce gwamnatin kasar ta Congo na shirin kaddamar da wani farmaki akan su, kuma ta tura sojojinta zuwa birnin Goma na gabashin kasar da sauran yankunan da ke karkashin ikon 'yan tawayen.

Ya kara da cewa matukar gwamnatin Kinsasha ta ki tasa hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta, to zasu nemi wakilan su dawo gida, kuma idan suka cigaba da kai musu hari ko shakka ba bu zasu kare kansu.

A cikin watan jiya ne Majalisar dinkin duniya ta saka wa 'yan tawayen kungiyar ta M23 takunkumi, jim kadan bayan sun kama garin na Goma.

Karin bayani