'Yan sanda a India sun tuhumi mutane biyar a Kotu

india
Image caption An yi zanga-zanga saboda yiwa matar fyade

'Yan sanda a Indiya sun tuhumi wasu mutane biyar da laiffukan yiwa wata maata fiyade tare da hallaka ta a cikin wata motar safa a birnin Delhi a watan jiya.

An tuhume su ne a wata kotu ta musamman da aka kafa domin gaggauta yi masu sharia saboda irin jan kafar da ake samu a irin wadannan karraraki a kasar.

Wadanda ake zargin dai ba su bayyana a kotu ba, kuma idan aka same su da laifi, za su iya fuskantar hukuncin kisa.

Ba a dai tuhumi mutum na shidda da ake zargi ba, har sai an gudanar da gwaje-gwaje a kansa domin tabbatar da ainihin shekarunsa.

Harin da aka kaiwa maatar dai, wadda daliba ce mai shekaru 23, ta haddasa jerin mummunar tarzoma a kasar ta India, inda galibi ba a hukunta masu cin zarafin maata.

Karin bayani