Za a tuhumi wadanda ake zargi da fyade

Mata masu zanga zanga a kasar Indiya
Image caption Mata masu zanga zanga a kasar Indiya

A kasar Indiya, ana dab da tuhumar wasu mutane biyar da ake zargi da hallaka wata daliba wacce aka yiwa fyade cikin wata motar safa a birnin Delhi na kasar.

A karshen mako ne dai dalibar mai shekaru ashirin da uku ta mutu sakamakon raunin da ta samu a lokacin da aka kai mata harin, lamarin daya haddasa kakkausar suka a cikin kasar.

Ana saran alkalan kotu ta musamman a birnin Delhi zasu zartar da hukunci ne bayan sun kammala yin nazari akan shafukka fiye da dubu na takardun da aka gabatar musu a matsayin shaida.

Wadannan takardu dai sun hada ne da bayanan da dalibar ta yi kafin mutuwarta.

Kuma bisa dokar kasar wajibi ne wadanda ake tuhuma su bayyana a gaban kotu a lokacin da za'a yanke musu hukunci, sai dai jami'an 'yan sanda sun ce ba za'a kawo mutanen gaban kotun ba, mai yiwuwa saboda dalilai na tsaro.

Matukar dai aka same su da aikata laifin, za'a yanke musu hukuncin kisa ne, koda yake mutum guda cikin wadanda ake zargi wani dan karamin yaro ne da bai balaga ba.

Tuni dai gwamnatin kasar ta ce tana shirin gabatar da sabuwar doka da ta tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da laifin aikata fyade tare kuma da fayyace dalla dalla irin laifuffukan da za'a rika yankewa hukuncin aikata fyade a kasar.