Fastoci: Fadar shugaban Najeriya ta tsame kanta

Fastar shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Image caption Jonathan ya ce bai umarci wasu su fara masa yakin neman zabe ba

Fadar shugaban kasar Najeriya ta musanta masaniya ko hannu a fastocin da aka lika na takarar shugaban kasar, Goodluck Jonathan a zaben shekarar 2015.

An dai lika fastocin ne a wasu manyan titunan Abuja, dauke da hotonsa da rubuce-rubucen da suka hada da cewa "Aso rock; Kwalelenku a shekara ta 2015".

Kakakin fadar shugaban kasar Reuben Abati ya shaidawa BBC cewa, shugaba Jonathan ba shi da hannu a lika fastocin, kana kuma bai umarci wasu su fara masa yakin neman zabe ba.

Mista Abati ya jaddada cewa shugaban ya ce a yanzu gwamnatin na maida hankali ne bisa ayyukan raya kasa.

Sannan da sauke nauyin da 'yan kasar suka dora masa, a matsayinsa na shugaban kasa.

'Yan adawa a kasar na sukar shugaban kasar game da fastocin, suna ganin ya yi wuri a fara maganar takarar zaben shekarar 2015 da shiga shekara ta 2013.

Inda suke ganin kamata ya yi gwamnatin Jonathan ta maida hankali kan inganta harkar tsaro a kasar.

Ita ma jam'iyya mai mulki, PDP ta nesanta kanta da batun manna fastocin yakin neman zaben na Jonathan.

Kakin jam'iyyar, Chif Olise Metu ya bayyana wa BBC cewa, PDP ba ta da masaniya game da manna fastocin.

Wata kungiya ce da ta fito daga kudu maso kudancin kasar, inda nan ne yankin da Shugaba Jonathan ya fito, ta yi ikirarin daukar nauyin fastocin.

Karin bayani