'Yan bindiga sun kashe mutane 4 a Adamawa

'Yan sandan Najeriya
Image caption Jami'an tsaro a Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro

Hukumomin tsaro a jihar Adamawa dake arewacin Najeriya, sun tabbatar da mutuwar mutane hudu da suka hada da soja da wani dan-sanda a wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai.

Harin dai ya auku a garin Song a daren ranar Laraba.

Sauran mutane biyun da aka kashen sun hada da wata dattijuwa da jikanta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, DSP Muhammad Ibrahim ya tabbatar wa da BBC mutuwar mutane hudun, yayin da wasu biyu kuma suka jikkata.

Maharan da ba a san ko su wanene ba sun kona caji ofis da kuma ginin sakatariyar karamar hukumar ta Song.

Maharan dai sun yi amfani da manyan bindigogi da rokoki da kuma bama-bamai wajen kai harin, inda suka yi kaca-kaca da gine-ginen na hukuma, bayan sun yi musayar wuta da jami'an tsaro.

Wani mazaunin garin ya ce sun ji karar harbe-harben bindiga.

Dan majalisar Gombe

A jihar Gombe mai makotaka da Adamawa kuma 'yan bindigan da suka sace dan majalisar dokokin jihar, kana shugaban kwamitin harkokin kudi na majalisar, Alhaji Jalo Ahmed Ganga sun sako shi jiya da daddare.

Wasu rahotanni na cewa sai da aka biya kudin fansa kafin su kyale shi.

Amma kakakin rundunar 'yan sandan jihar Gombe, DPS Fwaje Attajiri ya ce ko magana da masu garkuwar da shi ba a yi ba, sun dai saki dan majalisar bisa radin kansu.

An dai sace dan majalisar ne a ranar Lahadin da ta gabata.