Shugaba Hugo Chavez na numfashi da kyar

Shugaba Hugo Chavez na kasar Venezuela
Image caption Shugaba Hugo Chavez na kasar Venezuela

Gwamnatin Venezuela ta ce har yanzu shugaba Hugo Chavez na fama da ciwon huhu, makonni uku bayan da aka yi masa tiyatar cutar kansa a Cuba.

A wata sanarwa, ministan watsa labarai na kasar ya bayyana cewa shugaba Chavez na fuskantar matsala wajen iya yin numfashi.

Ministan ya kara da cewa ya zama wajibi ga Mr Chavez ya rika bi sau da kafa ka'idojin jinyar da likitoci a kasar Cuba suka shimfida masa.

Sanarwar ta biyo bayan sukar da gamayyar jam'iyun adawa na kasar suka yi ne dangane da abin da suka kira rufa-rufar da gwamnati ke yi game da halin lafiyar shugaban kasar.

Bisa tsari dai kamata yayi a rantsar da Mr Chavez na wa'adin mulki karo na biyu nan da mako guda biyo bayan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Oktoba, sai dai bisa ga dukkan alamu ba shi da koshin lafiyar dawowa gida domin a rantsar da shi.

'Yan adawa a kasar dai sun ce suna bukatar a tura wata tawagar likitoci ta musamman zuwa birnin Havaza na kasar Cuban domin tantance halin da shugaban kasar ke ciki.