Amurka ta soki Google kan Koriya ta Arewa

Google
Image caption Google ne kamfanin neman bayanai a intanet mafi girma a duniya

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta soki shirin da shugaban kamfanin matambayi baya bata na Google ke yi na ziyartar kasar Koriya ta Arewa.

Kawo yanzu dai Kamfanin na Google ya ki ya tabbatar da ziyarar, to amma ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Kudu ta ce tana sane da cewar Eric Schmidt na shirin kai wata ziyarar kashin kansa zuwa kasar da suka ce tana mulkin kama-karya.

Korea ta arewa na daya daga cikin kasashen duniya da har yanzu kamfanin na Google bai kai can ba.

Amma ana sa ran shugaban kamfanin na Google Eric Schmidt zai kai ziyara ta musamman kasar a 'yan makwanni masu zuwa.

Ziyara ce ta kashin kansa

Zai kai ziyarar ne tare da tsohon gwamnan Mexico Bill Richardson wanda ya dan sha zuwa birnin Pyongyang a baya.

Sai dai har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa Mr. Eric zai kai ziyara Pyongyang ba.

Duk da cewa sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta karfafa gwiwa a kan amfani da intanet da kuma kimiyya a matsayin abubuwan da ke da matukar muhimmanci a harkokin diplomasiyya, ma'aikatar cikin gidan Amurka ta soki ziyarar da Mr Eric, inda ta bayyana cewa ziyarar ba za ta taimaka ba.

Korea ta arewa ta kaddamar da roka mai cin dogon zango a watan Disambar shekarar da ta gabata, ba tare da la'akari da hana tan da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ba.

Kakakin ma'aikatar cikin gida ta Amurka Victoria Nuland, ta ce ziyarar da Mr Eric zai kai Korea ta Arewa ta kashin kansa ce, ba da yawun gwamnatin Amurka ba ne, kuma ba wani sako da zai isar daga gwamnatin kasar.

Karin bayani