An sallami Malala daga asibiti

Malala Yousufzai
Image caption Malala ta bar asibiti

An sallami matashiyar nan 'yar Pakistan Malala Yousufzai, wacce 'yan Taliban suka harba a ka, bisa kamfe da ta ke na bunkasa ilimin mata, daga asibitin da ake kula da ita a Burtaniya.

Likitoci sun ce za ta cigaba da murmurewa ne a gidan wucin gadin da iyayenta suka koma a yankin tsakiyar Ingila.

Daga bisani kuma za ta sake komawa asibiti dkomin yi mata aiki a kokon kanta.

Harbin dalibar dai a watan Oktoba ya haddasa cece-ku-ce a Pakistan da ma duniya baki daya.

Wakilin BBC yace da alamun dai Malala za ta tare a Burtaniya dindindin bayanda mahaifinta ya samu aikin diplomasiyya na shekaru uku a birning Birmingham.