Wanne taimako ka ke baiwa kasarka?

Nmfuk
Image caption 'Yan Najeriya musulmai daga sassan Burtaniya da dama ne suka halarci taron

Wani abu da ya fito fili a babban taron kungiyar musulmi 'yan Najeriya mazauna Burtaniya na shekara ta 2012, shi ne bukatar kowanne mutum ya tashi tsaye domin yin wani abu da zai taimaka wurin ci gaban al'ummarsa.

"Tashi tsaye ka tallafawa kasarka ko ka samau shiga cikin wadanda suka bada gudummawa wurin inganta rayuwar jama'a," a cewar Dr Datti Ahmad, shugaban majalisar wanzar da shari'ar musulunci a Najeriya.

Kusan duka bakin mahalatta taron ya zo daya wurin cewa al'amura basa tafiya daidai a Najeriya musamman a arewacin kasar, kuma a don haka akwai bukatar sauyi.

Taron wanda ya samu halartar 'yan Najeriya musulmai maza da mata daga sassan Burtaniya daban-daban, ya mayar da hankali ne kan yadda kawar da talauci da kyakkyawan shugabanci zai kawo karshen tashe-tashen hankula a Najeriya. Naziru Mikailu

"Idan babu shugaba nagari...."

Sai dai abin tambayar anan shi ne su wanene da alhakin tabarbarewar al'amura a arewacin Najeriya dama kasar baki daya? Mafiya akasari sun dora alhakin hakan ne kan shugabanni - sai dai wasu na ganin idan bera na da sata, to daddawa ma na da wari.

A cewar tsohon ministan Abuja Dr Aliyu Umar Moddibo, hanya daya tilo da za ta taimaka wurin bunkasa tattalin arziki da kawar da talauci, ita ce fadada hanyoyin samun kudaden shiga maimakon dogaro da man fetur kacal.

Sai dai da dama daga cikin mahalatta taron sun dora alhakin matsalolin da ake fama da su ne kan rashin shugabanci nagari, sai dai Dr Moddibo ya ce: "Idan bera na da sata, to daddawa ma na da wari," wato suma jama'ar gari na da nasu laifin.

Amma a ganin Sheikh Isa Ali Fantami, na jami'ar ATBU a Najeriya: "idan babu shugaba nagari mai tsoron Allah to ba za a taba samun adalci da kwanciyar hankali ba.

Idan shugabanni suka kwatanta adalci, to babu shakka za a samu ci gaba da zaman lafiya," a cewar Sheikh Fantami, yana mai bayar da hujjoji daga Alkur'ani mai girma.

Wacce gudummawa kake baiwa kasarka?

Image caption An tafka muhawara kan wadanda ke da alhakin tabarbarewar al'amura a Najeriya

"Daga cikin ayyukan da kungiyar ta 'yan Najeriya musulmai a Burtaniya ke mayar da hankali a kai shi ne gudanar da ayyukan lafiya kyauta da daukar nauyin yara marayu a wasu sassan kasar domin ganin cewa sun samu kulawa kamar sauran yara".

Tambayar a nan ita ce, me muke yi domin tallafa wa al'ummarmu, kuma ta yaya za mu shiga a dama da mu wurin tabbatar da ci gaban kasarmu?

Babu shakka kowa yana da rawar da zai taka, musamman wurin taimakawa da irin basirar da Allah ya hore masa ta hanyar tallafawa sauran jama'a musamman samari masu tasowa da masu karamin karfi don ganin cewa sun taso a kan tafarkin da ya dace.

"Babbar matsalarmu a Najeriya ita ce gazawa wurin tashi tsaye domin nuna rashin amincewa da barna da gwagwarmaya wurin tabbatar da shugabanci nagari. Kuma lallai ne muyi wannan idan muna so mu kai labari," a cewar Dr Datti Ahmad.

Karin bayani