Tattaunawa kan rikicin Sudan da Sudan ta Kudu

Tattaunawa tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu
Image caption Tattaunawa tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu

A ranar Juma'a ne shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta kudu zasu tattauna kan rikicin dake tsakanin kasashen wanda ke dab da zama yaki biyo bayan samun 'yancin kai da Sudan ta kudun ta yi a shekarar 2011.

Rahotanni sun bayyana cewa za'a yi tattaunawar ce a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha saboda rikicin da kasashen ke yi akan Iyakoki.

Ana dai kyautata zaton cewa shugaba Omar al Bashar na Sudan da takwaransa Salva Kiir na Sudan ta kudu zasu tattauna ne akan hanyoyin da za'a bi don aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a watan Satumbar da ya gabata.

Sai dai wasu na ganin cewa mai yiwuwa babu wani sauyi da za'a gani a tattaunawar da shugabannin kasashen biyu zasu yi bayan zargin da hukumomin Sudan ta Kudu suka yi a baya bayan nan cewa Jamhuriyar Sudan ta kaddamar da hare hare a jihar Bahr el-Ghazal dake kudancin kasar.