Hugo Chavez zai ci gaba da mulkin Venezuela

Mataimakin shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro
Image caption Mataimakin shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro

Mataimakin shugaban kasar Venezuela ya bayyana cewa shugaba Hugo Chavez zai ci gaba da zama akan karagar mulki koda kuwa bai sha rantsuwar kama aiki ba a ranar goma ga wannan watan kamar yadda aka tsara.

Mr Chavez wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Oktoban shekarar data gabata na wa'adin mulki karo na biyu, na fama da jinya ne a kasar Cuba na cutar Kansa a huhunsa bayan da aka yi masa tiyata karo na hudu.

A hira da yayi da gidan talbijin na kasar dauke da kwafi na kundin tsarin mulkin kasar a hannunsa, mataimakin shugaban kasar Venezuelan Nicolas Maduro ya ce za'a iya rantsar da Mr Chavez a wata rana ta dabam a harabar kotun kolin kasar.

Sai dai wata 'yar Majalisa daga bangaren 'yan adawa ta maida martani a shafin Twitter tana mai cewa matukar Majalisar dokokin kasar ta kasa samun bayani gamsasshe game da yanayin lafiyar shugaban kasar nan da ranar goma ga wannan watan, to kuwa kamata yayi majalisar ta bayyana shi a matsayin wanda baya nan don kama aiki.

Wannan mataki dai ka iya sa a gudanar da wani sabon zaben shugaban kasa cikin kwanaki talatin.

Kimanin wata guda kenan da ba'a sake jin duriyar shugaba Hugo Chavez ba tun bayan daya tafi kasar Cuba don a yi masa tiyata, inda wasu daga cikin mukarrabansa suka amince cewa yanayin jikinsa ya yi tsanani.