Likitoci a Kaduna sun yi barazanar dakatar aiki a jihar

Gwamnan jihar Kaduna Alh Muktar Ramalan Yero
Image caption Gwamnan jihar Kaduna Alh Muktar Ramalan Yero

A Najeriya, kungiyar likitoci ta kasar shiyyar Jahar Kaduna ta yi barazanar janye ayyukanta baki daya ko kuma takaita yawan sa'o'in da likitoci ke gudanar da ayyukansu a jihar matukar gwamnati ba ta dauki kwakkwaran mataki ba na kawo karshen kashe kashen 'ya'yanta da wasu mutane da ba'a san ko su wanene ba keyi a jahar musamman a garin Zaria.

Kungiyar wacce a ranar asabar din nan ta yi jana'izar daya daga cikin 'ya'yanta da wasu 'yan bindiga suka harbe a garin Zaria, na nuna damuwa ne a bisa karuwar wannan matsalar.

Shugaban kungiyar likitoci reshen jihar Kaduna Dr Usman Baffa Aliyu ya shaidawa BBC cewa daga watan Mayu zuwa Disambar bara an halaka mata kwararrun Likitoci guda uku.

To sai dai rundunar 'yan sanda a jahar ta bayyyana cewa ta yi nisa wajen binciken al'amarin.