Magoya bayan Hugo Chavez sun nuna hadin kai

Magoya bayan shugaba Hugo Chavez
Image caption Magoya bayan shugaba Hugo Chavez

Magoya bayan shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez sun nuna hadin kai yayin da ake ci gaba da bayyana shakku game da yiwuwar murmurewar shugaba Chavez daga jinyar da ya ke fama da ita.

Tuni dai majalisar dokokin kasar ta zabi Diosdado Cabello, wani na hannun daman shugaban kasar a matsayin shugaban Majalisar.

Matukar Mr Chavez ya kasa halartar bukin rantsar da shi da aka shirya gudanarwa a ranar alhamis mai zuwa, Mr Cabello ka iya tsintar kansa a matsayin shugaban kasar Venezuelan na rikon kwarya.

Yayin da gwamnati ke neman a dage ranar rantsar da shugaban kasar don bashi damar murmurewa, a bangare guda kuma 'yan adawa na bukatar Mr Chavez ne ya sauka daga mulki wanda zai bada damar a gudanar da wani sabon zabe.