'Yan bindiga sun kashe akalla mutane shida a Zamfara

Kanar Sambo Dasuki
Image caption Hare haren 'yan bindiga a arewacin Najeriya

A Najeriya hukumomi a Jahar Zamfaran arewacin Najeriya sun tabbatar da cewar wasu 'yan bindiga sun kai hari a kauyen Makera dake birnin Magaji da asubahin ranar asabar, kuma 'yan bindigar sun kashe akalla mutane shida a wurare daban daban, tare da jikkata wasu

Hukumomin sunce 'yan bindigar sun yiwa garin dirar mikiya ne akan babura da kuma mota, kuma yawan su zai kai talatin

Rahotanni sun ce 'Yan bindigar sun kuma yi artabu da 'yan banga masu aikin samar da tsaro a kauyen, bayan da 'yan bindigar su ka budewa mutane wuta a cikin wasu masallatai biyu a Kauyen na Makera.

Sai dai hukumomin sun ce ba a yi nasarar cafke kowa daga cikin 'yan bindigar ba.

Karin bayani