Shugaba Asad ya yi tur da 'yan adawa

Bashar Asad
Image caption Bashar Asad ya yi wa al'ummar Kasa jawabi

A jawabi na farko, da yayi wa 'yan kasarsa kai tsaye tun watan Yuni, shugaban Syria Bashar al-Assad ya yi tur da 'yan adawar da ya kira 'yan ta'addan da kasashen waje ke marawa baya.

Shugaba Assad ya kuma yi tayin warware rikicin kasar ta hanyar tattaunawa.

Mr. Assad ya baiyanawa magoya bayansa cewa a shirye ya ke a warware matsalar ta hanyar kiran wani taron sulhu, wanda zai rubuta sabon tsarin mulkin kasar.

Jagororin 'yan adawa da dama dai sun yi watsi da jawabin na Mr. Assad a matsayin ta gina ba ta shiga ba.

'Yan adawa sun yi watsi da jawabin Shugaba Asad

Tuni dai 'yan adawar Syria su ka yi watsi da jawabin na Shugaba Assad.

Wani wakili a majalisar hadaka ta dakarun 'yan adawan Syria, Haitham al-Maleh yace ba za su taba tattaunawa da Mr. Assad ba.

Ministan harkokin wajen Turkiyya kuwa, Ahmet Davutoglu yace babu abinda shugaba Assad ya yi face maimaita zantuttukan da ya saba.

Sakataren harkokin wajen Burtaniya ma William Hague yace shugaba Assad ne musabbabin rikicin da ya mamaye kasar.

Kungiyar gamayyar Turai kuma ta nanata matsayinta cewa tilas ne shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa.

Karin bayani