Sepp Blatter ya soki matsayin da Boateng ya dauka

Image caption Sepp Blatter na FIFA

Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, FIFA, Sepp Blatter ya ce dan wasan kungiyar kwallon kafa ta AC Milan Kevin-Prince Boateng ya aikata ba daidai ba da ya fice daga filin wasa bayan 'yan kallo sun furta masa kalaman wariyar launin fata.

Mista Blatter ya ce hakan ba maslaha ba ce, sannan ya kara da cewa kungiyoyi ka iya fuskantar asarar wasa idan suka yi koyi da Boateng da sauran 'yan wasan AC Milan yayin wani wasan sada zumunta a Italiya.

Wakilin BBC ya ce Mista Blatter ya ce kamata ya yi 'yan wasa su kai kara wajen alkalin wasa, kuma kamata ya yi a ragewa kungiyar da magoya bayanta suka aikata laifin maki.

Karin bayani