Za a rantsar da Mahama na Ghana

Image caption Za a rantsar da Shugaban kasar Ghana, Mahama

Zababben shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama za a rantsar da shi a ranar Litinin bayan da ya samu nasarar zabe a watan Disambar bara.

John Mahama ya samu sama da kaso hamsin cikin dari abin da ya bashi nasara zaben da ya ke kud da kud da abokin karawar sa.

J'amiyyar adawa dai ta kalubalanci zaben a gaban kotu; amma hakan ba zai hana rantsuwar a yau ba.

Mr Mahama dama ya kasance shugaban kasa tun lokacin da tsohon shugaban kasar Atta Mills ya mutu a watan Yulin bara.

Za a rantsar da shi a matsayin shuagaban kasa a gaban shugabannin kasashen Afrika goma sha daya har da shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonatahan, Shugaba Jacob Zuma na Afrika ta kudu da kuma Jakaya Kikwete na Tanzaniya.

Haka kuma Jamiai daga Birtaniya da Amurka da Sin za su halarta.

Karin bayani