Paparoma ya nemi a tsoma baki a Syria

Wasu 'yan gudun hijirar Syria
Image caption Wasu 'yan gudun hijirar Syria

Paparoma Benedict ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen abun da ya kira kisan gillar da ya ki ci ya ki cinyewa a Syria, kafin , kamar yadda ya bayyana, kasar ta durkushe.

A jawabinsa na shekara-shekara ga jami'an Diplomasiyya dake fadarsa ta Vatican, Paparoman ya yi tsokaci a kan halin kaka-na-ka yin da fararen hula ke ciki a kasar ta Syria.

Sannan ya sabunta kiraye-kiraye na tsagaita bude wuta da tattaunawar zaman lafiya.

Kalaman nasa dai sun zo ne kwana daya bayan da shugaban Syriar, Bashar al Assad ya gabatar da wani shirin zaman lafiya a Syriar, amma ya yi watsi da yiwuwar tattaunawa da 'yan tawaye.

Duka Amurka da Burtaniya da ma Tarayyar Turai sun yi watsi da kamalan na Mr Assad.

Karin bayani