Kasar Australia na fama da gobara

Image caption Gobara a Australia

Hukumar kashe gobara a kasar Australia ta ce New South Wales na fuskantar gobarar daji mafi muni a cikin tarihin yankin.

Wurare fiye da dari ne suka kama da wuta,inda kuma akwai wurare ashirin da daya da aka kasa cimmusu wadanda ba a kai ga kashe su ba a Jihar da ta fi kowacce al'umma.

Gobarar ta kazanta, inda take da matukar hadari kasancewar ana iska mai karfi, da busassun itatuwa sannan yanayi na kusantar maki 40 bisa ma'aunin celsius.

An ja kunnen Mazauna yankin Kudancin Australia kan gobarar mai munin gaske wadda iska mai yawa da kuma yanayin zafi ke rurata.

Masu kashe gobarar dai na ta kokarin murkushe wutar dajin mai girman gaske a wuraren dake makwabtaka da Victoria; sannan kuma an nuna damuwa sosai kan garin Tasmania wurin da yafi kamuwa a karshen mako.

A wata sanarwar da Hukumar kula da yanayi ta Australia ta fitar ya nuna cewar a kowacce rana ta kwanaki shidan farko na shekara ta 2013 an samu zafi sosai da ya shiga tarihi.

Wanannan ne dai karo na farko a Australia ma'aunin zafi ya haura maki talatin da tara cikin dari na Celsius a kwanaki biyar a jere.

Karin bayani