Faransa za ta kara caji kan kamfanonin intanet

Amazon
Image caption Amazon, Google, da Apple na daga cikin kamfanonin da abin zai shafa

Gwamnatin Faransa za ta bullo da hanyoyin cajar manyan kamfanonin internet irin su Amazon da Google da kuma Apple, saboda suna amfani da na'urar sadarwa mai yawa.

Ministan sadarwa na Faransa Fleur Pellerin ya bayyana cewa, bukatar amfani da kayayyakin wadannan kamfanoni ta haifar da karin samar da ababan more rayuwa, a saboda haka dole su biya.

Sai dai kuma kamfanin Google ya ce tuni ya biya makudan kudade a kan hanyoyin sadarwarsa.

A wani labarin kuma, wata kotu a birnin Texas na Amurka ta yi watsi da karar da wata daliba ta shigar wacce ta nuna adawa da shirin makarantarta ta sanya wata na'ura a bajon da dalibai ke sawa.

Dalibar ta ki sanya bajon ne bisa dalilan addini.

Makarantar na amfani da na'urar jikin bajon ne domin gano daliban da ke zuwa da kuma masu fashi.

Hukuncin kotun na nufin a yanzu dole dalibar ta sanya bajon ko kuma ta sauya makaranta.

Karin bayani