Ana artabu tsakanin Mali da 'yan tawaye

Image caption 'Yan tawaye a Mali

Rahotanni daga Mali sun ce wani sabon rikici ya barke tsakanin dakarun gwamnati da masu tsattsauran ra'ayin Islama a tsakiyar kasar.

An ba da rahoton cewa dakarun gwamnati sun harba makaman artillary a kan masu tsattsauran ra'ayin ne da ke nausawa kudanci, yankin da ke karkashin ikon gwamnatin.

Masu tsattsauran ra'ayin sun kwace ikon arewacin kasar bayan wani juyin mulkin soja a watan Maris din shekarar da ta gabata.

Za a fara tattaunawa tsakanin gwamnatin Mali da 'yan tawayen kasar a makociyar kasar Burkina Faso sati mai zuwa.

Karin bayani