Praministan Turkiyya na ziyara a Nijar

Praminista Erdogan na Turkiyya
Image caption Praminista Erdogan na Turkiyya

Praministan Turkiya Recep Tayip Erdogan ya fara wata ziyarar yini biyu a Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijar.

Ranar Talata ya isa Nijar daga kasar Gabon, a ci gaba da ziyarar da yake yi a wasu kasashen Afrika.

Dazu shugaba Erdogan ya yi wata ganawa da shugaba Issoufou Muhammadou, inda suka tattauna kan wasu muhimman batutuwa da zasu shafi kasashen biyu.

Daga cikin tawagar praministan har da 'yan kasuwan Turkiyya.

Kasar Turkiyya dai ta dade tana hulda da kasashen Afrika da dama, kuma tana da galibin ofisoshin jakadancinta ne a kasashen dake kudu da hamadar Sahara.

A gobe ake sa ran Praminista Erdogan zai wuce Dakar, babban birnin Senegal.

Karin bayani