'Ana kokarin kafa kungiyar dakile yawan bindigogi a Amurka'

giffords
Image caption Tsohuwar 'yar majalisa Gabrielle Giffords

Tsohuwar 'yar majalisar dokokin Amurka Gabrielle Giffords wacce ta sha-da kyar bayan wani harbi da wani dan bindiga yai mata a 'ka' , za ta kaddamar da wata kungiya da nufin dakile amfani da bindiga ta mummunar hanya.

Misis Gabriel da maigidanta sun ce lokaci yayi da ya kamata ace ayi wani abu game da mallakar bindiga a Amurka.

Wakilin BBC yace "Manufar kungiyar ma'auratan biyu, shine tara kudade domin dakile kamun-kafar da ake yi a siyasance, a kan batun mallakar bindiga, da kuma nuna goyan baya ga mallakar bindigar daya dace".

A makon daya gabata Misis Giffords da maigidanta, sun kai ziyarci garin New Town dake jihar Connecticut, inda aka kashe kananan yara ashirin da kuma wasu manya shida a wata makaranta, a watan Disambar da ya gabata.

Karin bayani