Ana bukatar dakarun NATO a Mali - AU

'Yan tawayen Mali
Image caption 'Yan tawayen Mali sun karbe iko da wasu manyan garuruwan dake arewacin kasar

Shugaban Tarayyar Afrika wato AU, Thomas Boni Yayi, ya yi kira da a tura dakarun NATO zuwa kasar Mali domin yakar 'yan tawaye a kasar.

Ya ce rikicin na Mali, batu ne da ya shafi kasashen duniya, don haka ya kamata dakarun Nato su kai dauki, kamar yadda suka yi a Afghanistan.

Sai dai ya ce, kasashen Afrika ne ya kamata su jagoranci duk wani mataki da za a dauka a Malin.

A watan da ya gabata ne majalisar Dinkin Duniya ta amince a tura dakarun kasashen Afrika 3,000 zuwa Mali.

Sai dai jami'an na Majalisar sun ce, ba sa sa ran za a tura dakarun kafin watan Satumbar shekarar nan.

Tuni kasashe da dama mambobin kungiyar ta NATO da suka hada da Amurka da Faransa suka yi alkawarin bada horo ga dakarun da za a tura Malin, sai dai ba su yi alkwarin tura nasu dakarun domin yakar 'yan tada kayar bayan ba.

Masu kishin Islama da 'yan tawayen Abzinawa sun kwace iko da arewacin Mali, yankin da ya kai girman kasar Faransa.

A wani yanayi na rudani da ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Bamako babban birnin kasar ta Mali.