An sako Italiyawa 3 da aka sace a Najeriya

Jirgin ruwa a kan teku
Image caption Ana samun karuwar fashin jiragen ruwa a gabar Tekun Guinea

'Yan fashin teku sun saki 'yan kasar Italiyan nan uku ma'aikatan jirgin ruwa, da suka kame a Najeriya a watan da ya gabata.

Ma'aikatar harkokin wajen Italiya ce ta tabbatar da hakan, sai dai ba ta yi karin bayani kan ma'aikacin jirgin ruwa na hudu dan kasar Ukrain da aka kama tare da su ba.

Wasu 'yan bindiga ne dai suka kutsa kai cikin jirgin ruwan mai suna MV Asso Ventuno, a lokacin da yake cikin Tekun yankin jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Sata da kuma garkuwa da mutane, batu ne da yake dada yin kamari a Najeriya.