Jirgin ruwa ya kama wuta a Legas

Tashar jiragen ruwa a Tekun legas
Image caption Tashar jiragen ruwa a Tekun legas

Wani jirgin ruwa dake dakon man diesel ya yi bindiga, kana ya kama da wuta a tashar jiragen ruwa dake Legas a Najeriya.

Al'amarin ya faru ne yayin da ake sauke man diesel daga jirgin, kuma mutane hudu sun jikkata.

Gobarar dai ta shafi ofisoshi da dama dake tashar jiragen ruwan ta Tin Can.

An dai samu nasarar kashe gobarar, kuma ana kokarin tantance girman barnar da ta janyo.

Hukumar agajin gaggawa ta kasar, NEMA ta shaidawa BBC cewa babu wanda ya mutu a sanadiyar al'amrin.

Najeriya na daga cikin manyan kasashen duniya dake samar da danyen mai, sai dai tana shigo da tataccen mai da sauran albarkatun man daga kasashen ketare.