Za a gina sabbin jami'o'i uku a arewacin Najeriya

ilimi
Image caption Ministar ilimi a Najeriya, Farfesa Rukayyatu Ahmed Rufa`i .

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta kafa sababbin jami'o'i a wasu jihohi uku da ke arewacin kasar.

Manufar shirin shine a samar da wuraren zurfafa karatu ga dubban daliban da ke kammala karatun sakandare a kowace shekara a kasar.

Kamar yadda Ministar ilimin kasar, Farfesa Rukayyatu Ahmed Rufa'i ta ce sanar, za a gina sabbin jami'o'inne a jihohin Kebbi da Zamfara da kuma Yobe.

A halin da ake ciki dai jami'o'in da ke kasar ba sa iya samar da guraben karatu ga sama da kashi goma bisa dari na daliban.

Karin bayani