An kama mutane da makamai a jihar Plateau

binciken jami'an tsaro a Nijeriya
Image caption binciken jami'an tsaro a Nijeriya

Hukumomin tsaro a Jihar Filaton Nijeriya mai yawan fama da rigingimu, sun bayyana kama wasu mutane tara da muggan makamai da kuma katunan shaida na wasu cibiyoyin gwamnatin jihar.

An kama mutanen ne jiya da dare dauke da manyan bindigogi cikin motoci a wasu kauyuka dake yankin Jos ta kudu inda rahotanni suka ce ko a jiya da daren ma mutane biyu sun rasa rayukansu a wani kwanton bauna.

Hukumar tsaro ta JTF a jihar ta tabbatar da kama mutanen, ta kuma ce tana ci gaba da bincike.

Jihar Pilato dai ta yi fama da rikici da ake dangantawa da kabilanci da kuma addini, lamarin da ya haddasa asarar rayuwa da dimbin dukiya.

Karin bayani