Majalisar Venezuela ta ce a dage rantsuwa

Image caption Shugaban Majalisar dokokin Venezuela, Diosdado cabello

Majalisar dokokin Venezuela ta amince da bukatar shugaba Hugo Chavez ta dage bikin rantsar da shi a kan kujerar shugabanci wanda aka tsara yi a ranar Alhamis.

'Yan majalisar sun kada kuri'ar ba shi isasshen lokaci domin ya murmure daga aikin da aka yi masa na cutar sankara a Cuba a watan da ya gabata.

Mataimakin Shugaban kasar Nicolas Maduro ya ce shugaba Chavez ba zai samu damar halartar bikin rantsarwar ba.

Jagoran 'yan adawa Henrique Caprile ya yi kira da a baiwa kakakin majalisar rikon mulkin kasar.

Karin bayani