An tarbi Jirgin Argentina da aka rike a Ghana

Image caption Shugaban argetina Cristina na murnar dawowar Jirginsu

ShugabaR kasar ARgentina Cristina Fernandez Ta yi marhabin da jirgin ruwaN da aka tsare fiye da watanni biyu a Ghana.

An rike jirgin mai suna libertaD ne saboda karar da wani kamfani ya kai kasar ta Agentina saboda ta kasa biyan bashin da ake bin ta shekaru goma da suka wuce.

Dubun dubatar al'umar kasar sun yi jerin gwano a gabar tekun Mardel Plata domin taron jirgin tare da gudanar da shagulgula.

Wakilin BBC ya ce jirgin ruwan ya samu kyakkyawar tarba a lokacin da ya isa Argentina.

Karin bayani