An kashe Kurdawa mata uku a Faransa

kurd
Image caption Sakine Cansiz na daga cikin wadanda aka kashe

An harbe wasu mata Kurdawa uku har lahira- da suka hada da wadda da ita aka kirkiri kungiyar 'yan gwagwarmayar Kurdawa ta PKK, Sakine Cansiz a Paris a wani abinda yansanda suka bayyana a matsayin kisan gilla.

Yansanda sun samu gawarwakinsu ne a wani Ofishi dake rufe a Cibiyar watsa labarai ta Kurdawa da sanyin safiyar ranar alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa, ana ganin girman Sakina Cansiz, amma kuma bata daga cikin shugabannin kungiyar dake tada kayar baya a Turkiyya kusan shekaru takatin da suka gabata.

A lokacin ziyarar da ya kai inda aka yi kashe kashen, ministan kula da harkokin cikin gidan Faransa, Manuel Valls, ya yi Allahwadai da alamarin inda ya bayyana shi da cewa mummunan aika aika ne.

Wadannan kashe kashen dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa an samu gagarumar nasara a tattaunawar da ake yi ta samun zaman lafiya tsakanin gwamnatin Turkiyya da shugaban kungiyar PKK Abdullah Ocalan, wanda a halin yanzu yake zaman wakafi na daurin rai da rai.