An kafsa fada tsakanin sojojin Mali da 'yan tawaye

mali
Image caption 'Yan tawaye ne keda iko a arewacin Mali

An yi kazamin fada a Mali, tsakanin dakarun kasar da kuma gamayyar kungiyoyin 'yan tawayen nan masu kaifin kishin Islama dake iko da garin Konna dake tsakiyar kasar.

Wani kakakin yan tawaye ya ce dakarunsa sun fatattaki dakarun gwamnati, sannan sun sake kwace iko da garin.

Kakakin sojin ya ki ya tabbatar ko musanta ikirarin.

Shi ne dai fada mafi girma tun lokacin da kungiyoyin masu kishin Islama suka kama arewacin kasar daga dakarun Gwamnati a cikin watan Afrilu a bara.

Masu aiko da rahotanni sun ce idan har garin ya shiga hannun 'yan tawayen, hakan zai kasance wani babban koma baya ga kokarin da sojojin Malin ke yi na hana yaduwar 'yan tawayen a cikin yankunan da gwamnatin Kasar ke iko da su.

Majalisar dinkin duniya dai ta amince da wani shiri na tura dakarun kasa da kasa zuwa Malin, mai yiwuwa a cikin watan Satumba, domin fatattakar 'yan tawayen.

Karin bayani