An yi zanga zanga bayan hare haren bam a Pakistan

Wani harin bam a Pakistan
Image caption Wani harin bam a Pakistan

Al'umar Yan Shi'ar da aka hara da hare haren bama bamai biyu a birnin Quetta ranar alhamis sun ki rufe wadanda suka mutu har sai soji sun karbi iko da birnin.

Wani shugaban yan Shi'a ya shedawa BBC cewar yana son wani tabbaci daga soji cewar za su kare al'umar.

Mutane fiye da 80 ne aka kashe sannan wasu da yawa suka samu raunuka a hare haren da aka kai a wani wurin wasan snooker a yankin yan shi'a.

Hare hare a kan yan shi'a yan tsiraru sun karu a cikin shekarun baya bayan nan.

Wata kungiyar 'yan gwagwarmayar Islama ta Lashkar-e-Jhangvi ta ce ita ce ta kaddamar da hare-haren.

Karin bayani