An kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Taswirar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Image caption Taswirar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Rahotanni daga Jumhuriyar Afrika ta Tsakiya sun ce wakilan gwamnati da na 'yan tawaye sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon mako guda kacal.

An cimma yarjejeniyar ne a rana ta biyu ta shawarwarin sulhu da ake yi tsakanin bangarorin biyu a Libreville babban birnin kasar Gabon.

'Yan tawayen wadanda suka kwaci yankin kasar mai yawa a watan da ya gabata, suna neman Shugaba Francois Bozize ne ya yi murabus.

A ranar Larabar da ta gabata ne suka nace a kan cewar sai lallai a gurfanar da Mr Bozize gaban Kotun duniya, game zargin shi da laifin cin zarafin bil-adama.

Rahotanni sun bayyana cewa kusan kashi tamanin da biyar na yankunan kasar na hannu 'yan tawaye ne wadanda suke bukatar shugaba Francois Bozize ya sauka daga kan mulki.