An amince da kafa gwamnatin hadaka a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Shugaban kasar Jamhuriyar tsakiyar Afirka, Francois Bozize
Image caption Shugaban kasar Jamhuriyar tsakiyar Afirka, Francois Bozize

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da kungiyoyin 'yan tawaye sun amince da kafa gwamnatin hadaka, a wani bangare na yarjejeniyar da suka cimma ta tsagaita wuta.

Sanarwar ta zo ne bayan an shafe kwanaki ana tattaunawar sulhu a Libreville, babban birnin Gabon.

A karkashin yarjejeniyar, Shugaba Francois Bozize, zai ci gaba da jan ragamar kasar har zuwa karshen wa'adin sa na shekara ta dubu biyu da goma sha-shida, za a kuma nada wani dan adawa a matsayin Prime Minista.

A watan jiya ne 'yan tawayen suka koma bakin daga a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar, tare da kame wasu garuruwa, har suka isa daf da Bangui babban birnin kasar.