Faransa ta daukar kara matakan tsaron cikin gida

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Image caption Shugaban kasar Faransa Francois Hollande

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ce an kara tsaurara matakan tsaron cikin gida, don kare harin daukar fansa daga 'yan tawaye masu kishin Islama.

Sojojin Faransa a tsakiyar kasar Mali na cigaba da kai hari ta sama a kan mayaka 'yan kishin Islama.

Mr Hollande din ya ce kasar Faransar ta samu gagarumin ci gaba a fafatawar, sai dai kuma da sauran runa a kaba.

A yayin da sojojin kasar ta Faransa ke ci gaba da kai farmakin, an kashe matukin wani karamin jirgin sama, kana kuma gwamnatin Mali ta ce an kashe sojojin ta goma sha-daya.

Shugaban Faransar Francois Hollande, ya ce za a kara sa ido kan gidajen mutane da ababan hawa domin tabbatar da tsaron.

Ya kuma jaddada yunkurin neman amfani dakarun kasashen Afirka, don ceto kasar ta Mali da dawo da martabarta, kamar yadda kwamitin tsaro ya zartas.

Kasar Brittaniya ma dai ta ce za ta taimaka da abubuwan sufuri na daukar dakarun da kayan yaaki zuwa Mali, to amma ba za ta bayar da sojojin da za su shiga fafatawar ba.