Zanga-zangar adawa da auren jinsi a Faransa

Jerin gwano a Paris
Image caption Jerin gwano a Paris

Akalla masu adawa da aure tsakanin jinsu guda, su dubu dari hudu ne suka gudanar da zanga-zanga a Paris domin rashin amincewa da kudirin gwamnati na halatta auren a Faransa.

Kimanin mutane dubu dari takwas ne suka shiga zanga-zangar, a cewar wadanda su ka shirya ta.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya sha alwashin halatta auren tsakanin jinsi guda nan da watan Yuni.

Mai magana da yawun wadanda suka shirya gangamin, fitacciyar mai wasannin barkwanci Frigide Barjot ta roki shugaba Francoise Hollande da ya sauya shawara.

Cocin katolika, da jagororin Musulmi, da kuma jam'iyyun masu ra'ayin rikau na matukar adawa da kudirin halatta auren jinsin tare da baiwa masu luwadi da madigo damar karba 'ya'ya daga gidan marayu su mai da su na su.

Karin bayani