Matsalar Fyade a India na karuwa

An kama wasu mutane shida a arewacin Indiya bisa zargin aikata wani sabon fyade a cikin motar haya, wannan karon a jihar Punjab.

'Yan sanda sun ce matar mai shekara ashirin da tara ta shiga motar haya ne ita kadai amma sai direban da kwandasta suka ki tsayawa a wurin saukarta, suka zarce wani gida inda suka gaiyato mazaje biyar suka yi mata fyade.

Yanzu haka an kama mutane shida daga cikin wadanda ake zargi da yin fyaden,yayin da ake ci gaba da neman mutum na bakwai.

Fyade da kisan kan da aka yiwa wata matashiya a motar haya, a watan jiya a garin Delhi dai ya jawo zanga-zanga da neman tsaurara dokokin fyaden a kasar ta Indiya.

Karin bayani