Ba zamu fasa kafa sansani ba - Netanyahu

Benjamin Netanyahu
Image caption Benjamin Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yace Isra'ilan ba za ta fasa aniyarta ta gina sabuwar unguwar Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna a gabar yammacin kogin Jordan ba, bayanda 'yan sandan kasar suka kori wasu Palasdinawa da 'yan kasashen waje da ke zanga-zanga, a filin da ake shirin fara ginin.

Mr. Netanyahu yace an tarwatsa masu fafutukar ne daga kan dutsen da su ka yi zaman dirshan, saboda gujewa faruwar tashin hankali.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta haramtawa Isra'ila yin ginin, wanda zai tare tsakanin birnin Qudus da gabar yammacin kogin Jordan.

A baya dai Isra'ila ta dakatar da shirin bayan da Amurka ta soki ginin, sai dai Mr. Netanyahu ya dawo da batun gina matsugunin bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta daga darajar Palasdinu.