Gobarar bututun mai ta hallaka mutane 30 a jahar Ogun

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Mutane akalla talatin ake fargabar sun mutu, sakamakon wata gobara da ta tashi a wani bututun man fetur na Areppo cikin jihar Ogun.

Bayanai daga hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, mai lura shiyyar kudu maso yammacin kasar sun tabbatar da cewa gobarar ta tashi a babban bututun man petur na Areppo dake jihar Ogun da har yanzu suke kan gudanar da bincike a kai.

Rahotanni sun rawaito cewa wutar ta tashi ne bayan da wasu masu satar man petur suka fasa bututun man, kuma akalla mutane talatin ne ake fargabar sun hallaka lokacin da suke kwasar ganimar man.

Wani babban jami'in 'yan sanda mai lura da shiyyar kudu maso yammacin Najeriya ya shaidawa manema labarai cewar gobarar ta tashi sakamakon gardamar da ta kaure tsakanin masu kwasar ganimar man, bayan da daya daga cikin ya fusata ya harba bindigar da ta tayar da gobarar.

Ko a tsakiyar watannin bara, wasu mutane sun fasa bututun man petur na Areppo dake cikin jihar Ogun, tare da hallaka wasu jami'an kamfanin man petur na Najeriyar NNPC, lamarin da ya haifar da karancin man petur din a fadin kasar.