'Yan Shia a Quetta na san a kafa dokar ta baci

Firaministan Pakistan, Raja Pervez Ashraf, na ganawa da 'yan Shia a garin Quetta da ke kudu maso yammacin kasar, wanda suka ce ba za su binne gawarwakin wadanda aka kashe musu a harin bom na ranar Alhamis ba har sai an kafa dokar ta baci a yankin.

Ya tattauna da su game da bukatar su ta ganin an tube gwamnansu an mika mulki hannun soji.

An dai gudanar da zanga-zanga a manyan biranen Pakistan irinsu Karachi, da Lahore, da kuma Rawalpindi domin rashin amincewa da harin bama-bamai biyun da ya hallaka akalla mutane casa'in.

Wata haramtacciyar kungiyar 'yan bindiga ta Sunni, Lashkar-e-Jhangvi ta ce ita ce ta kai harin.

Karin bayani