Ministan kudi na Iraqi ya tsallake rijiya da baya

Wani harin bom a kasar Iraqi
Image caption Wani harin bom a kasar Iraqi

Ministan kudi na Iraqi ya tsallake rijiya da baya a wani yunkuri da aka yi na hallaka shi.

Ministan Rafa al-Essawi yana tafiya ne cikin ayarin wasu motoci a yammacin Bagadaza, lokacin da wani bam da aka dana bakin hanya ya tarwatse.

Babu dai wanda aka raunata, amma an lalata motoci da dama.

Mr al-Essawi din ne kan gaba a rikicin siyasar dake gudana, wanda ya assasa boren da mabiya Sunni 'yan tsiraru suka yi ma Prime Minister Nouri Al-Malki.