'Kate Middleton za ta haihu a watan Yuli'

Yarima William da Kate
Image caption Kate zata haihu a watan Yuli mai zuwa

Gidan sarautar Burtaniya ya ce ana saran matar Yarima William wato Kate Middleton, za ta haihu a watan Yuli mai zuwa.

A watan da ya gabata ne aka bayyana cewa Catherine, wacce ita ce Duchess ta Cambridge, ta samu juna biyu.

Jami'ai sun ce tana samun sauki daga laulayin da ta yi fama da shi, wanda ya sa aka kwantar da ita a asibiti.

Jariri ko jaririyar da za a haifa dai, zai kasance na uku a sahun masu jiran hawa karagar mulkin.

Masu lura da al'amura na ganin sanarwar wani tabbaci ne na cewa da daya za ta haifa, ba tagwaye ba.

Karin bayani