Tattalin arzikin kasar Girka zai bunkasa - Lagarde

Shugabar hukumar IMF Lagarde da Ministan Kudi na kasar Girka
Image caption Shugabar hukumar IMF Lagarde da Ministan kudi na kasar Girka Venizelos

Shugabar Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF, Christine Lagarde ta ce tattalin arzikin kasar Girka zai kara bunkasa a cikin wannan shekarar.

Tace zai kara bunkasa fiye da da, kamar yadda hasashen wannan shekarar ya nuna.

Lagarde ta kuma yi hasashen samun ci gaba a sauran kasashe masu amfani da kudin Euro cikin wannan shekarar.

Fiye da kashi daya bisa uku na mutanen kasar ba su da aikin yi, sannan tattalin arzikin kasar a durkushe yake tun a shekarar 2008.

Amma Mrs. Lagarde ta ce Girka ta yi namijin kokari wajen warware gibin kasafin kudin ta, don haka tattalin arzikin zai zarce yadda aka yi hasashen cigabansa a shekara ta 2003.

Kasar Girka ta fuskanci matsalolin harkokin kudi da suka hada da kangin basussuka.