Sojan Faransa na biyu ya mutu a Somaliya. In ji Al-Shabaab

Wasu mayakan al-Shabaab a Somaliya
Image caption Wasu mayakan al-Shabaab a Somaliya

Kungiyar 'yan kishin Islama ta Al-Shabaab a Somalia ta ce sojan Faransa na biyu ya rasu bayan yunkurin kubutar da wani dan Faransar da ya ci tura.

Al Shabab ta wallafa wani hoto a intanet da ta ce gawar sojan na Faransa ce, shimfide kusa da wasu makamai da kuma kayan aikin soja. Praministan Faransa Jean-Marc Ayrault, ya bayyana nuna gawar a matsayin wani mataki na nuna rashin sanin ya kamata.

Faransa ta ce ta tura dakaru zuwa Kudancin Somalia ranar Juma'a a kokarin kubutar da wani jami'inta na leken asiri. Hakan na faruwa ne yayinda Faransar ta tsoma baki a fadan da ake yi da 'yan Kishin Islama a kasar Mali.

Karin bayani