Mutane sama da tamanin sun mutu a Aleppo

Jami'ar Aleppo, bayan harin
Image caption An kai harin ne lokacin da dalibai ke zana jarabawa

Wani abu mai karfin gaske ya fashe a jami'ar birnin Aleppo na kasar Syria a daidai lokacin dalibai ke rubuta jarabawa, inda ya rutsa da mutane da dama.

Majiyoyi da yawa ciki har da gwamnan birnin - sun ce fiye da mutane tamanin sun mutu.

Wasu hotonan bidiyo da aka wallafa a internet, sun nuna yadda harin ya lalata wani bangare na jami'ar, da kuma gawarwakin mutane warwatse a kan hanya.

Wadanda suka shaida lamarin, da kuma kungiyoyin masu fafutuka sun ce wani bam da jiragen yakin gwamnati suka jefa ne ya haifar da fashewar.

Ita kuma gwamnati ta dora alhakin lamarin ne kan 'yan tawaye.

Ana yi wa jami'ar kallon wuri mafi kwanciyar hankali a garin na Aleppo wanda ya dade yana fama da tashin hankali.