Faransa ta samu goyon bayan kasashen duniya a kan Mali

Shugaban Faransa
Image caption Sojin Faransa na fafatawa da 'yan tawayen Mali

Kasar Faransa ta samu cikakken goyon baya daga kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dangane da shirinta na yin amfani da karfin soja wajen murkushe 'yan tawaye masu kaifin kishin Islama a Mali.

Jakadan Faransa a Majalisar, Gerard Araud, ya shaida wa kwamatin Sulhun cewa kasar sa tana so ne dakarun kasashen Afirka su karbi ragamar yunkurin da ake yi na fatattakar masu kaifin kishin Islaman nan ba da dadewa.

Mista Araud ya kara da cewa daukar matakin soja ya zama wajibi saboda lamarin ya shafi kasancewar Mali a matsayin kasa, da ma kwanciyar hankali kasashen yammacin Afirka.

Ministan harkokin wajen kasar, Laurent Fabius, ya ce Faransa kadai ba za ta iya daukar wannan mataki ba a kan Mali.

Dakarun Afirka za su isa Mali nan gaba kadan

Da alama ma'aikatan diplomasiya sun fi mayar da hankali ne kan yadda cikin gaggawa dakarun kasashen Afirka za su shiga kasar ta Mali don taimaka wa dakarunta wadanda ba su da isassun kayayyakin yaki.

Da ma dai shirin Majalisar Dinkin Duniya shi ne a tura sojin kasashen Afirka kasar, sai dai kudurin da ya bayar da wannan umarni ya amince ne da a dauki watanni ana shiryawa kafin kai hari kasar; kuma za a yi hakan ne yayin da a gefe guShugaban Faransada ake kokarin tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan tawaye don samun mafita a siyasance.

Mista Araud ya ce yana sa ran dakarun kasashen Afirka za su isa kasar ta Mali a makon gobe.

Karin bayani