Jiragen yaƙin Faransa sun kai hari kan 'yan tawaye a Gao

Sojojin Faransa a Mali
Image caption Faransa ta ce burinta shi ne samar da zaman lafiya a Mali

Jiragen yaƙin Faransa sun yi lugudan wuta kan 'yan tawaye a garin Gao na arewacin Mali, wanda ke da muhimmanci ga 'yan tawayen.

Wadanda suka shaida lamarin sun gaya wa BBC cewa an kai hari kan filin saukar jiragen sama na Gao, kuma da dama daga cikin 'yan tawayen sun fice daga garin.

Tun da farko dai wani janar ɗin soji na Najeriya Shehu Usman Abdulkadir, ya shaida wa BBC cewa rundunar farko ta dakarun ƙasashen Yammacin Afrika za ta isa Mali nan da 'yan kwanaki kaɗan.

Ya ce za su je ƙasar ne domin tallafawa a yaƙin da Faransa ke jagoranta da 'yan tawaye wadanda ke iko da arewacin ƙasar.

Da yake magana a lokacin wata ziyara a Dubai, shugaban Faransa Francois Hollande, ya ce ƙasarsa ba ta son daɗewa a Mali.

Ya ce sojojin Faransar za su fice ne kawai daga Mali, lokacin da suka cimma burinsu, wanda shi ne samar da zaman lafiya a ƙasar da tabbatar da tsarin siyasa da kuma kawar da barazanar 'yan ta'adda. .

Karin bayani